ALAQAR HIZBOLLAH DA SOJOJIN QASSEM SOLEIMANI
Ita dai wannan alaqa ta wadannan sojoji guda biyi alaqace wacce ta dade kuma ake aiki tare domin kawo karshen zaluncin yahudawan isra'el da masu goya masu baya.
Sojojin hezbolla sun kasance rundunar da ake lissafawa a dunia wajan sanin yaki da kwarewa da kokarin samarwa da kasarsu ta lebnon ''yanci da kariya daga sharrin yahudawan isra'ela. Kamar yanda yake sanannen abune cewa kasar isra'el basu da wani buri daya wuce mallakar kasashen dake makota dasu, domin zalunci da rashin imani kuma akokarin samun abinda suke so suna zubar da jinin al'ummar da suke son mamayewa da duk wani nau'i na zalunci wanda ya sabawa dan'adam taka.
Yahudawan na kasar isra'el suna yiwa musulmai yankan rago da kwace duk wani abu wanda musulman suka mallaka kamar yanda yake sananne a tarihi irin yanda suke yiwa al'ummar palestine, da sauran kasashen duniya.
Alaqar hezbollah da sojojin na qassem soleimani alaqace wacce suke aiki tare suke kuma fatattakar yahudawan isra'el da america daga kasashen musulmai kamar syria iraq yemen da kuma palestine.
Babu wata runduna da azzalumai suke tsoro kamar wadannan rundunoni guda biyu, hakanne yasa america da isra'el suka shirya makirci da makarkashiya wajen ganin sun shahadantar da daya daga jagoran wannan runduna Shahid Qassem soleimani da kuma abokin aikinsa na rundunar hashdushsha'abi dake kasar iraq.
........Abu zahra...........